Gwamnatin jihar Sakkwato ta rufe hanyoyin sadarwa a kananan hukumomi 14 daga cikin 23 na jihar, a wani mataki na dakile Yan bindiga a fadin jihar.
Gwamnan jihar Aminu Tambuwal ya sanar da matakin a yau Litinin.
A wata hira da Sashen Hausa na Muryar Amurka wato VOA, Gwaman Tambuwal ya ce, jihar ta samu amincewar Ministan Sadarwa Isah Pantami, kafin aiwatar da dokar a yau Litinin.
Ya ce, yankunan karamar hukumar da abin ya shafa sun fi fuskantar hare -haren yan bindiga a jihar.
KARANTA WANNAN LABARIN:Sanwo Olu ya Sanya hannu kan dokar Hana kiwo a Bainar jama’a
Wannan na zuwa ne biyo bayan nasarar da ake tunani an samu a Zamfara mai makwabtaka da jihar ta Sokoto.
Kazalika Gwamna Tambuwal ya ce, biyo bayan haramcin da aka yi a Zamfara, yan bindiga sun tsananta kai hare -hare a Sokoto, inda yayi nuni da cewa, matakin ya yi nasara a Zamfara, wanda a sakamakon haka yan bindiga ke tserewa daga jihar zuwa Sokoto.
“Sakamakon nasarorin da sojoji ke samu a jihar Zamfara, yan bindigar suna tserewa zuwa Sokoto,” in ji gwamnan Tambuwal
Tambuwal ya bayyana wasu kananan hukumomin da lamarin ya shafa kamar haka: Dange Shuni, Tambuwal, Sabon Birni, Raba, Tureta, Goronyo, Tangaza da Isa da dai sauran su.
A wani labarin Kuma na daban.
Akalla dalibai bakwai ne aka ruwaito sun jikkata lokacin da daliban kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar Filato a ranar Litinin suka gudanar da zanga zanga kan dage jarabawar su ta semester.
Mahukuntan makarantar sun dage jarabawar saboda wani yajin aikin da malaman makarantar suka fara.
Daliban da ke shirin rubuta jarabawar, sun gamu da kofar makarantar gaba daya a rufe, inda daliban suka fusata suka kuma fito kan tituna don yin zanga zanga amma rahotanni sun bayyana cewa wasu ‘yan daba ne suka yi awon gaba da gilashin motoci.
Masu zanga zangar sun toshe hanyar Yakubu Gowon, babban titin da ke shiga da fita daga Jos tare da haddasa cunkoson ababen hawa cikin sa’o’i da yawa.
Da yake magana da manema labarai daya daga cikin daliban, Mista Tindak Theophilius, ya ce daliban da suka ji rauni suna karbar magani a wani asibiti a Jos.Ya ce wasu daga cikinsu marasa lafiyar asma ne da ba za su iya jurewa barkonan tsohuwa da aka harba don tarwatsa daliban ba.
Ya bayyana matakin da hukumar ta dauka na dage jarabawar a matsayin wani yunkuri na takaita tafiyarsu ta ilimi “Mun zo makaranta yau da safe don fara jarabawar mu kawai sa muka samu labarin cewa malaman mu na yajin aiki tun ranar Juma’a.
“Mun shafe sama da shekaru uku a cikin semester daya kawai saboda kullen COVID-19 amma galibi saboda yajin aikin da malaman mu suka fara.” Muna ci gaba da biyan kudin masaukin mu, kudin makaranta, da sauran kashe kudi. tsufa kuma lokacin da muka kammala karatu, ba za mu iya samun ayyukan yi ba saboda tsufa, ”in ji John.
Duk kokarin da mukayi najin ta bakin Mista John Ramadan na sashen hulda da jama’a na cibiyar a lokacin hada wannan rahoton ya ci tura.
Comments 1