Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin fara shimfiɗa aikin bututun iskar gas mai tsawon kilomita 614 a Arewacin Najeriya.
Bututun iskar gas din mai zai taso daga Ajaokuta dake jihar Kogi, ya biyo ta babban birnin tarayya Abuja, kana ya biyo ta Kaduna, daga karshe kuma ya dire a Kano.
Da yake lura da kaddamar da aikin ta fasahar kiran Bidiyo wato (video conference call) a ranar Talata daga fadar gwamnati tarayya a Abuja, Buhari ya ce shimfiɗa bututun abu ne mai muhimmanci ga ‘yan Najeriya, don haka ba za a bari ya lalace ba.
Buhari wanda ya ce aikin zai taimaka wajen bunkasa harkokin tattalin arzikin Najeriya ya ce wajibi ne a yi dukkan mai yiwuwa wajen aiwatar da aikin yadda aka tsara shi, a kuma kammala shi a kan lokaci.
An bude aikin ne daga fuskoki guda biyu, inda Gwamnan Kogi Yahaya Bello ya wakilci Buhari ta bangaren Ajaokuta tare da Shugaban Kamfanin NNPC, Mele Kolo Kyari.
Daga ɗaya bangaren kuwa, Gwamnan jihar Kaduna, MalamNMalam El-Rufai sun kaddamar da aikin daga Rikachikun tare da Karamin Ministan Albarkatun Mai.