By Abbas Yakubu Yaura
Karamin Ministan Ayyuka da Gidaje, Alhaji Muazu Sambo, ya ce gwamnatin tarayya ta bayar da tallafin Naira biliyan 3 na Sukuk don samar da hanyar Numan zuwa Jalingo a jihohin Adamawa da Taraba a shekarar 2022.
Sambo ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin da yake duba ayyukan hanyoyin gwamnatin tarayya a tsakanin jihohin Taraba da Adamawa.
Masu Jiran Gado 20 Sun Fara Tururuwar Neman Darewa Kujerar Sarautar Alaafin Na Oyo
Ya ba da tabbacin cewa da zarar an shiga asusun Sukuk, za a sami gagarumin ci gaba a wurin ginin.
“Titin Numan zuwa Jalingo mai tsawon kilomita 103 yana cikin babbar hanyar Maiduguri zuwa Calabar.
“Sashin hanyar mota bata iya bi kuma ba a yarda da ita ba don hanyar ita ce kadai hanyar da ke tsakanin Arewa da Kudu a kan yankin Arewa maso Gabas na kasar,” in ji Sambo.
Ministan ya ce ba zai zargi dan kwangilar da yin tafiyar hawainiyar akan aikin ba.
A cewarsa, saboda rashin isasshen kasafin kudin da aka yi a baya da kuma zuwan annobar COVID-19 da ta shafi ci gaban aikin.
Sai dai ya ce da irin yadda ake samun ingantattun kudade a halin yanzu, ana sa ran dan kwangilar zai yi hidimar kayan aikin sa da kuma dagewa wajen yin aikin ginin.
Ya ce idan har aka gano kamfanin ba shi da karfin kammala aikin, gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen soke kwangilar tare da sake bada ita ga wani kamfanin da ya cancanta.
A lokacin da take yiwa Ministan bayanin yadda ake gudanar da aikin a hanyar Numan zuwa Jalingo, wata babbar Injiniya a wurin, Maria Zirrah, wacce ta wakilci babban jami’in kula da ayyuka na tarayya na Adamawa, ta ce rashin tsaro da rashin kayan gini da kudade ne suka haddasa tafiyar hawainiya na aiki a kan lokaci.
Har ila yau, Injiniya ayyuka na kamfanin Deux Project Limited, dan kwangilar aikin Numan-Jalingo, Frank Koshihuk wanda ya yi magana a madadin dan kwangilar, ya ce hauhawar farashin kayayyaki, kudade, rashin tsaro sune manyan kalubalen da aikin ginin yake fuskanta.
Koshihuk ya yi alkawarin cewa da zaran an inganta tsarin samar da kudaden da ake kashewa, za a kammala aikin cikin watanni takwas.
NAN ta ruwaito cewa ministan ya kuma duba aikin titin Zing-Yakoko-Monkin a Taraba a ziyarar aiki ta kwanaki biyu days kai.
Aikin gyaran hanyar Numan zuwa Jalingo an baiwa kamfanin Deux Project Nigeria Ltd akan kudi Naira biliyan 11.6 a watan Maris din shekarar 2017 wanda za’a kammala a watan Yulin shekarar 2019.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa gwamnatin tarayya ta saki Naira biliyan 1.5bn ga dan kwangilar wanda ya aiwatar da kashi bakwai cikin dari na aikin.