Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun Laraba da Alhamis a matsayin ranakun hutu don bukukuwan Karamar Sallah.
Ministan harkokin cikin gida Mallam Rauf Aregbesola shine ya sanar da hakan a Litinin.
Cikin wata sanarwa daga Babban Sakatare Ma’aikatar Dakta Shuaibu Belgore, ta taya al’ummar musulmi fuskantar wannan lokaci na Sallah.
Ministan ya bukaci al’ummar Musulmi da su yi amfani da lokacin wajen gudanar da addu’o’in zaman lafiya a kasar nan.
Daga bisani sai ya ja hankalin jami’an tsaro da su tashi tsaye don dakile duk wasu miyagun mutane da za su kawo rudani wa kasar