Gwamnatin tarayya ta ba da kwamgilar gina tituna 70 daga shekarar 2017 zuwa yau a Arewata tsakiya, a wani mataki na bunkasa ci gaban gine-gine a kasarnan.
Aganabah Bola, mukaddashin Daraktan lura da manyan titunan Arewa tasakiya na ma’aikatar ayyuka, shi ne ya bayyanawa manema labarai hakan a garin Patigi dake karamar hukumar Patigi a jihar Kwara.
Ya kuma bayyana hakan ne a yayin da yake amsa tambayoyin da aka yi masa bayan kammala ziyarar duba ayyukan da titi da gwamnatin tarayya ke yi a jihar.