Gwamnatin tarayya ta tabbatar da cewa ta shirya tsaf don kaddamar da tsarin yanar gizo na 5G a kasar don saukaka lamuran intanet.
Mataimakin Shugaban Hukumar Sadarwa ta kasa NCC Farfesa Umar Danbatta shi ya sanar da haka a ranar Juma’a yayin sauraron koken jama’a game da siddabarun da ake bukata don tabbatar da wannan tsari.
Farfesa Danbatta ya jaddada cewa tuni hukumar NCC ta mika takardar bukatar samar da tsarin ga Ma’aikatar Sadarwa da Habaka tattalin arzikin yanar gizo wato NITDA wanda a yanzu haka kawai take jiran sahalewar ta don fara aiwatar da aikin 5G din.
Tun a wata Mayu ne da NCC ta sanya hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna da hukumar kula da na’urar sama jannati ta satellite don bunkasa harkar 5G din a Nigeria.
A tsokacinsa Shugaban Hukumar Kwamishinoni a hukumar NCC Farfesa Adeolu Akande ya bayyana cewa shugabanni da dama sun yunkura don ganin cewa tsarin 5G ya tafi yadda ya kamata musamman a watanni ukun farkon shekara ta 2019.
Ya ce kuma tuni kasashe irin su Amurka da Koriya ta Kudu da sauran manyan kasashe suka aiwatat da tsarin intanet na 5G a ƙasashensu, lamarin da ya sa a yanzu hala suke gudanar da lamuran intanet cikin ruwan sanyi.