Babban Bankin Najeriya (CBN) ya fara ɗaukar matakan ƙayyadewa da kuma lura da farashin kayan da ke shigowa Najeriya daga ƙasashen waje.
CBN ya ce zai riƙa yin hakan ne ta hanyar sabon tsarinsa na tantance farashin hajojin da yake ba wa ‘yan kasuwa masu shigo da su daga ƙetare canji.
“Kamar yadda ake yi a ƙasashen duniya, nan take CBN ya fara aiwatar da tsarin tantance farashin kayan ƙasashen waje domin hana tsawwala ko karya farashin kayan a cikin ƙasar nan”, kamar yadda ya sanarwar ta bayyana.
https://dimokuradiyya.com.ng/cbn-ta-daina-bai-wa-masu-shigo-da-madara-tallafi/
Saƙon da bankin ya fitar a ranar Litinin 24 ga watan Agusta ya ce hakan na daga, “ƙoƙarin bankin na tabbatar da amfani da canjin da yake bayarwa ta yadda ya dace da kuma hana tsawwala farashi ko karɓar canji fiye da sau ɗaya da a ƙarshe suke komawa a kan ‘yan Najeriya masu sayen kaya.
“Ana umartar dukkannin manyan ‘yan canji da su daina buɗe ‘Form M’ ga masu karɓar canjin ta hannun dillalai ba kai tsaye ba”, injin sanarwar ta Daraktan Kasuwanci da Canjin Kuɗi na babban ƙasar nan CBN, O. S. Nnaji ya bayyana.