Daga: Uzairu Lawal Rigasa
Gwamnatin tarayya ta jaddada kudirinta na kammala dukkan ayyukan tituna da ke gudana kafin watan Yunin 2023.
Mista Jide Ode-Martins, daraktan bincike da kididdigar tsare-tsare na ma’aikatar ayyuka da gidaje ta tarayya ne ya bayyana haka a lokacin bude taron majalisar ayyuka na kasa karo na 28 a ranar Litinin a Kano.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kenya: Madigun ‘Yan Adawa Odinga Ya Kalubalanci Sakamakon Zaben Shugaban Kasa A Kotu
Taron mai taken “kayan aiki, lokacin kammalawa”.
Ode-Martins ya ce ainihin taron shi ne tabbatar da cewa masu ruwa da tsaki sun taru tare da yin shawarwari kan batutuwan da suka shafi ababen more rayuwa musamman kan tituna.
A cewarsa, gwamnati mai ci ta tanadi abubuwa da dama don ganin an kammala dukkan ayyukan tituna kafin watan Yunin 2023.
“Mafi yawan tituna da gadoji wannan gwamnatin za ta kammala su. An bude ayyukan hanyoyi biyar zuwa shida a yankin Arewa maso Yamma, wasu kuma a Arewa ta Tsakiya.”
“Wasu daga cikin ayyukan titin sun hada da titin Nguru-Gashuwa, a jigawa muna da titin Shuwarin – Bauchi, titin Shuwarin-Maiduguri; a Arewa – Ta Tsakiya, muna da gadar Owetto, wacce ta hada jihohin Benue da Nasarawa.”
“Aiki ne da yawancin mu a nan mun kware sosai kuma muka himmatu wajen yi a wannan shekara.”
“Za a kammala titin Legas zuwa Ibadan da gadar Neja ta biyu,” in ji Ode – Martins.
Hakazalika kwamishinan ayyuka na jihar Kano, Alhaji Idris Wada wanda babban sakataren ma’aikatar Alhaji Ahmed Salisu ya wakilta ya ce taron na da matukar muhimmanci.
“Dukkan ayyukan raya ababen more rayuwa za a kammala su nan ba da jimawa ba,” in ji Wada.NAN
A wani labarin kuma Yan bindiga Sun Kashe Mamallakin Otal, Sun Yi Garkuwa Da Abokin Sa
Wasu ’yan bindiga, a ranar Lahadin da ta gabata, sun kai farmaki wani otal mai suna 16 HOUR Hotel da ke unguwar Alomilaya na garin Ganmo, ta hanyar Ilorin a Jihar Kwara, inda suka kashe mai Otel din Mai shekaru 45 mai suna Kayode Akinyemi.
A cewar jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Okasanmi Ajayi a Ilorin a ranar Litinin, manajan otal din mai suna Emmanuel Olushila Ojo ya samu munanan raunuka a yayin harin da ake kyautata zaton kisan gilla ne, kuma a yanzu haka yana karbar magani a babban asibitin Ilorin.