Daga: Uzairu Lawal Rigasa
Dan takarar shugaban kasar Kenya da ya sha kaye, Raila Odinga, ya shigar da kara a gaban babbar kotun kasar a ranar Litinin yana kalubalantar sakamakon zaben da aka gudanar a ranar 9 ga watan Agusta wanda ya kai ga samun nasarar abokin hamayyarsa William Ruto.
Odinga wanda gogaggen dan adawa ne wanda ya yi takara tare da goyon bayan shugaba Uhuru Kenyatta da kuma jam’iyyar da ke mulki, ya yi watsi da sakamakon zaben, yana mai bayyana shi a matsayin “rashin gaskiya.”
KARANTA WANNAN LABARIN: Zargin Ta’addanci: ‘Yan sandan Pakistan Na Tuhumar Tsohon Faraministan Kasar
Ya sha kaye a hannun Ruto da kusan kuri’u 230,000 – kasa da kashi biyu cikin dari.
Dan siyasar mai shekaru 77 ya shigar da kwafin takardar koken ne da kyar sa’a daya kafin wa’adin kotun ta amince da shi da karfe 2 na rana (dai dai da karfe 11: 00 a agogon GMT).
An shigar da kwafin kan layi da safiyar ranar, a cewar wani memba na kungiyar lauyoyin sa.
Daruruwan magoya bayansu ne suka yi ta murna yayin da aka sauke kwalayen shaidu da dama daga wata babbar mota a wajen kotun.
Daniel Maanzo, memba na kungiyar lauyoyin Odinga ya shaidawa AFP cewa “Muna da fata cewa mun gabatar da kara mai kyau kuma za mu yi nasara.”
Ko da yake an gudanar da ranar zaben cikin lumana, amma sanarwar da sakamakon zaben mako guda da ya gabata ya haifar da zanga-zangar nuna bacin rai a wasu yankunan Odinga kuma ana fargabar cewa rikicin da ya kunno kai zai iya haifar da tashin hankali a kasar da ke da tarihin tashe tashen hankula a bayan zaben.
Tun daga shekara ta 2002, kowane zaben shugaban kasa a Kenya yana haifar da cece-kuce, inda sakamakon zaben na bana ya haifar da cece-kuce a cikin hukumar zabe mai zaman kanta (IEBC) wacce ta sa ido kan zaben.
Odinga, wanda ya tsaya takararsa karo na biyar na neman babban mukami, a makon da ya gabata ya ce alkaluman da hukumar ta IEBC ta sanar ba su da tushe balle makama kuma dole ne kotu ta soke su.
A cewar wani kwafin koke mai shafuka 72 da kamfanin dillancin labaran AFP ya gani, tawagar Odinga ta yi zargin cewa shugaban hukumar ta IEBC Wafula Chebukati ya kasa kirga kuri’u kusan 140,000.
Sakamakon haka, Ruto “bai cika sharuddan tsarin mulki na kashi 50% da 1 na sahihin kuri’un da aka kada ba” – bukatar bayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben.
Yanzu haka dai alkalai na da kwanaki 14 don yanke hukunci. Idan sun ba da umarnin sokewa, dole ne a gudanar da sabon zabe cikin kwanaki 60.
– ‘Muna Son Adalci‘ –
Magoya bayan Odinga sun fara taruwa a wajen kotun sa’o’i kadan kafin isowarsa, suna bushe bushe da raye-raye da kuma daga allunan da ke dakuke da rubutu “Adalcin Zabe Yanzu!” da “Muna son adalci a yanzu”.
“Dole ne Odinga ya yi nasara domin mu sami shillings 6,000 ($ 50) da aka yi alkawari a cikin littafinsa,” in ji wani mutum, sanye da kambi da aka yi da tsire-tsire wanda ke magana a kan tallafin kuɗi na wata-wata ga gidaje masu rauni.
Wani mutum – dauke da Littafi Mai Tsarki sanye da manya-manyan koren gilashin – ya durkusa cikin addu’a yayin da ‘yan sanda ke gadin harabar kotun.
Ana kuma sa ran alkalai za su yi la’akari da wasu kalubalen da ake fuskanta kan sakamakon, inda magatakardar kotun ya shaida wa manema labarai cewa kotun ta riga ta karbi kararraki biyu da wani mai zabe da wata kungiya mai zaman kanta ta shigar.
Hukumar ta IEBC dai ta fuskanci matsin lamba kan ta gudanar da zabe mai tsafta bayan fuskantar kakkausar suka kan yadda ta gudanar da zaben watan Agustan shekarar 2017, wanda shi ma Odinga ya kalubalanci shi a kotu.
Kotun ta soke wancan zaben a karo na farko ga Afirka tare da ba da umarnin sake gudanar da zaben wanda Odinga ya kauracewa zaben. Mutane da dama ne suka mutu a lokacin da ‘yan sanda ke murkushe masu gudanar da zanga-zanga.
A wani al’amari mai ban mamaki jim kadan kafin bayyana sakamakon zaben na bana, hudu daga cikin kwamishinonin hukumar ta IEBC sun zargi shugaban Chebukati da gudanar da wani aiki na “shara” kuma daga baya ya ce adadin bai taka kara ya karya ba.
Chebukati ya yi watsi da ikirarin, yana mai dagewa cewa ya gudanar da aikinsa bisa ga dokar kasa duk da ” tsoratarwa da cin zarafi”.
– Rarraba Ra’ayi –
Masana harkokin shari’a sun rabu kan ko Chebukati na bukatar goyon bayan kwamishinonin domin bayyana sakamakon, inda lauyan tsarin mulkin kasar Charles Kanjama ya shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP cewa akwai “wani shubuha” da ke tattare da batun.
A baya Odinga ya ce an yi masa magudi a zabukan shekarar 2007,2013 da 2017, kuma ana kallon sakamakon zaben a matsayin wani gwaji na balaga da dimokuradiyya a yankin gabashin Afirka.
A fagen yakin neman zabe, dukkan jiga-jigan biyu sun yi alkawarin warware duk wata takaddama a kotu maimakon a kan tituna.
Tun bayan bayyana sakamakon zaben, Odinga ya yabawa magoya bayansa da suka “kwantar da hankalinsu” yayin da Ruto ya dauki matakin sasantawa tare da yin alkawarin yin aiki da dukkan shugabanni.
Rikicin zabe mafi muni a Kenya ya faru ne bayan zaben shekarar 2007, inda sama da mutane 1,100 suka mutu a rikicin siyasa da ya hada da kabilu masu gaba da juna.
Idan kotun kolin ta amince da sakamakon, Ruto zai zama shugaban kasar Kenya na biyar tun bayan samun ‘yancin kai daga Birtaniya a shekarar 1963, inda ya karbi ragamar mulkin kasar da ke fama da hauhawar farashin kayayyaki, da rashin aikin yi da kuma gurgunta fari.AFP
A wani labarin kuma An Caccaki Shirin Gwamnatin Tarayya Na Haramta ASUU
Ana ci gaba da yin suka daga ‘yan Najeriya kan shirin gwamnatin tarayya na haramta kungiyar malaman jami’o’i (ASUU).
Rahotanni sun bayyana cewa Gwamnatin Tarayya na shirin rushe kungiyar malaman jami’o’in Najeriya ASUU saboda gazawarta na janye yajin aikin da ta dauki tsawon lokaci tana yi bayan wasu tayi da gwamnatin tayi kungiyar ta yi watsi da su.