Babban Sakatare, Hukumar Nakasassu ta Kasa, James David Lalu, ya ce akwai shirin na musamman domin kafa cibiyoyin nakasa a jami’o’in tarayya guda hudu dake Nigeria.
Lalu, a cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, Mbanefo JohnMichaels, ya fitar jiya Lahadi, ya ce, an yi hakan ne domin a mayar da cibiyoyi masu nakasa a jami’o’i domin janyo Nakasassu a jiki.
Ya fadi hakan ne yayin da ya karbi bakuncin Mataimakin Shugaban Jami’ar Nnamdi Azikiwe dake Awka a Jihar Anambra, Farfesa Charles Esimone.
Ya lissafa jami’o’in da za’a Gina cibiyoyin Nakasassu kamar haka: Jami’ar Usman Dan Fodio, Jami’ar Ilorin, Jami’ar Ahmadu Bello da kuma Jami’ar Nnamdi Azikiwe.
KARANTA WANNAN LA ARIN: Hukumar FRSC ta ja hankalin Matafiya kan Babbar Hanyar Kogi
Ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya umarci hukumar ta PWD, da ta fito da dabarun da za su sanya jami’o’in su yi aiki da su domin dauke su a kan titunan dake fadin kasar nan.