Bayan kashe Naira biliyan 276 kan gyaran matatun na man fetur daga 2015 zuwa 2018, gwamnatin tarayya na shirin sake kashe ƙarin Naira biliyan 600 domin gyaran su daga farkon 2021.
Gwamnatin ta kashe Naira biliyan 152 kan gyaran matatun daga shekarar 2013 zuwa 2017, idan za a iya tunawa.
Rahotanni sun bayyana cewa lalacewar matatun man na daga cikin dalilan raguwar kuɗaɗen shigar gwamnati da ƙarin farashin man fetur a cikin gida.
Bayan cire hannun gwamanti a harkar mai a baya-bayan nan da ya haifar da ƙarin farashin, Minista a Ma’aikatar Albarkatun Mai, Timipre Sylva ya ce ƙarin ba shi da makawa saboda farashin mai a kasuwar duniya ne ke yanke yadda za a sayar da shi a cikin gida.
Sai dai masana harkar sun ce da matatun na aiki to da tattalin arziƙin ƙasar nan bai samu matsala sosai ba, hatta a lokacin annobar Korona.
Wasu na ganin gyaran matatun na iya fitar da Najeriya daga ƙangin shigo da mai daga ƙetare, wasu kuma na ganin matatun “sun tsufa sosai da za a yi ta gyarawa”.
Don haka suka shawarci gwamnati, duba da yadda kimiyya da fasaha ke sauyawa, da ta gina sabbin matatu na zamani masu matsakaitan girma.
Yayin da ake ta kai ruwa rana kan ƙarin farashin mai, gwamnatin tarayya na ƙoƙarin kwantar da ƙurar da cewa za ta farfaɗo da matatun su riƙa aiki da aƙalla kashi 90 na ƙarfinsu cikin shekara uku.
Shugaban Kamfanin Mai na Kasa (NNPC), Mele Kolo Kyari ya ce matatun ƙasar nan guda huɗu (Kaduna, Warri, Fatakwal da Indorama, Eleme) na da jimillar ƙarfin tace ganga 444,000 na mai a kullum.
A jawabinsa, ya ce da gangan aka rufe su saboda rashin yi musu cikakken gyara da manyan garambawul.
Duk da cewa an kashe sama da biliyan N276 wurin gyaran su daga shekarar 2015, Kyari ya ce rashin yin gyaran da ya dace ya rage ƙarfin matatun, wanda hakan ne ya kawo buƙatar a yi musu muhimman gyare-gayre da garambawul.
“Ana buƙatar kowace matata ta yi aiki na aƙalla kashi 90 ds ƙarfinta.
“Dakatar da gyare-gyaren ya sa babu yadda za a yi su iya aiki na kashi 90 din ƙarfinsu.
“Mun kiyasta za su yi aiki na kashi 60 amma kuma hakan ba zai biya buƙata ba.
“Muna so su yi aiki yadda ya kamata ne shi ya sa za mu yi musu cikakken gyara”, inji shi.
Ya ce a watan Mayun 2020 aka samu injiniyoyi na cikin gida daga Kamfanin Ayyukan Injiniya na Kasa (NETCO/KBR) ƙarkashin NNPC da za su yi aikin matatun mai na Warri da Fatakwal.
Za a kashe Dala biliyan 1.5 (Naira biliyan 576.75) wurin gyaran matatar Fatakwal wanda aka ƙulla yarjejeniyar biya ta hanyar bayar ds ɗanyen mai a maimakon kuɗi.
Aikin, mai suna Project Eagle ya samu goyon baya daga Bankin Shige da Fice na Afirka (Afreximbank).