Daga: Abbas Yakubu Yaura
Gwamnatin Yobe a ranar Asabar ta ce ta kashe sama da Naira biliyan 2.9 wajen siyan takin zamani daga shekarar 2019 zuwa yau 2022.
Dakta Mairo Amshi, kwamishiniyar ma’aikatar noma da albarkatun kasa ta jihar ce ta bayyana hakan a wani taron karawa juna sani na ministoci, ranar Asabar a Damaturu.
KARANTA WANNAN LABARIN: Buhari Zai Halarci Taron Majalisar Dinkin Duniya Karo Na 77
Ta ce an kashe Naira biliyan 1.5 daga cikin kudin wajen siyan tan 3,000 na takin NPK 20:10:10 a shekarar 2021.
Amshi ta ce ana ci gaba da rabon takin da kuma sayar da takin ne ta budaddiyar kasuwa akan kudi naira 13,000 kan kowanne buhu.
Kwamishiniyar ta kuma ce an kashe Naira biliyan 1.4 wajen siyan tan 7,500 na NPK 15:15:15 a shekarar 2020.
Kwamishiniya ta kara da cewa, an sayar wa manoman kayan a kan Naira 5,000 kan kowanne buhu, wanda ke nuna tallafin kashi 40 cikin 100.
Ta bayyana cewa a shekarar 2019, gwamnati ta kashe Naira miliyan 882 wajen siyan taraktoci 40, inda ta ce an ba su a matsayin rance ga manyan manoma kan Naira miliyan 11 kowanne, wanda za a biya cikin shekaru hudu.
Amshi ta ce jihar tare da hadin gwiwar kungiyar agaji ta Red Cross (ICRC) sun yi wa shanu da tumaki da awaki da karnuka sama da miliyan 1.2 allurar rigakafin a cikin wannan lokaci.
Sannan kwamishiniyar ta ce shirin bunkasa kiwo na jihar yana samun tallafin likitocin dabbobi 135, masana kimiyyar dabbobi 47, asibitocin dabbobi guda biyar da kuma ofisoshin kiwon dabbobi na Area 17 a fadin jihar.
Ta ce jihar tare da hadin gwiwar ma’aikatar noma da raya karkara ta tarayya (FMARD) sun kafa cibiyoyin raya dabbobi a wuraren kiwo na Jakusko/Nasari, Badegana da Gurjaje.
Kazalika tace kayayyakin da aka riga aka samar a cibiyoyin sun hada da rijiyoyin burtsatse, madatsun ruwa, asibitin dabbobi, wurin ciyar da abinci, tafkunan kifi, hanyoyin shiga, wutar lantarki, ingantattun magunguna da wuraren tattara madara da dai sauransu.
A cewar kwamishiniyar cibiyar bincike da kiwo (LIBC) da jihar ta kafa daidai wa daida a Nguru domin bunkasa noman dabbobi.
A kokarinta na bunkasa noman ban ruwa, ta ce, ya zuwa yanzu an samu sama da hekta 2,000 na fili domin fara aikin noman LAVA na shekarar 2022 a wasu sassan jihar.
Amshi ta ce jihar tare da hadin gwiwar jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, sun kafa cibiyar binciken samar da dabbobi ta kasa (NAPRI) a yankin Arewa maso Gabas a Damaturu.
Ta kara da cewa jihar ta samu amincewar shiga shirin Gwamnatin Tarayya na Tallafin Dabbobin na (Shirin L-Pres).NAN
A wani labarin kuma, Dole APC Tayi Ƙwaƙƙwaran Motsi, Kafin Babban Zaɓen 2023 – Tinubu
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu ya bukaci ‘yan jam’iyyar a shiyyar Arewa maso Gabas da su kara kaimi kafin zaben 2023.
Ya bayyana haka ne a Gombe ranar Asabar a wajen liyafar daurin auren Misbahu Yahaya dan Gwamna Inuwa Yahaya.