Daga Ibrahim Hassan Hausawa
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zai bar Najeriya, domin halartar taron majalisar dinkin duniya karo na 77, (UNGA77). Kamar yadda PremiumTimes ta ruwaito
Mai bashi shawara bangaren yada labarai Me Femi Adesina ne ya bayyana hakan, a wata Sanarwa da ya fitar a yau.
KARANTA WANNAN LABARI: Dole APC Tayi Ƙwaƙƙwaran Motsi, Kafin Babban Zaɓen 2023 – Tinubu
Jaridar Dimokuraɗiyya ta rawaito cewa sanarwar ta ce an tsara cewa shugaba Buhari zai gabatar da jawabi gaban mahalarta taron, a ranar 21 ga watan nan na Satumba.
Baya ga wannan taron, shugaba Buhari zai kuma halarci wani taro kan tattalin arzikin kasashen duniya da Najeriya, wanda nan ma zai gabatar da jawabi.
Kungiyar dai an samar da ita ne hadin gwiwa da Najeriya domin haɓaka tattalin arzikin mambobinta.
Daga cikin yan rakiyar shugaban sun haɗar da mai dakin sa Aisha Buhari, da Wasu daga cikin Gwamnoni da ministocinsa.
Kuma ana saka ran zai dawo Najeriya a ranar 26 ga watan Satumba.
A WANI LABARIN KUMA: Burtaniya Na Neman Iyalan Wasu Yan Najeriya Ruwa A Jallo Bayan Iyayensu Sun Mutu
Gwamnatin Birtaniya ta wallafa jerin sunayen ‘yan Najeriya 56 da suka mutu suka bar dukiya mai tarin yawa a kasar Amma ba tare da an gano makusanta da za su gaji wannan dukiyar ba.
Jaridar BusinessDay da ake wallafawa a kasar, ta ce daga cikin dukiyoyin da mutanen suka mutu suka bari har da gidaje, wadanda a karkashin dokokin Birtaniya, matukar aka share tsawon shekaru 30 daga ranar da mai ita ya mutu amma ba a gano magadan mamancinsa ba, dukiyar za ta zama mallakin baitil-mali.
Comments 1