Gwamnatin jihar Zamfara ta yabawa majalissar dokokin jihar bisa amincewa da dokar kare hakkin jama’a data zama doka
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai da daraktan hulda da manema labarai na majalisar, Kwamared Nasiru Biyabiki ya sanyawa hannu tare da raba wa manema labarai a Gusau, inda ya ce an yabawa majalisar kan ci gaban da aka samu kwanan nan.
KARANTA WANNAN LABARIN: FG Ta Ankarar Da Jami’an Lafiya Kan Yiwuwar Bullar Kyandar Biri a Kauyuka
A cewar sanarwar, kwamishiniyar jin kai, kula da bala’o’i da ci gaban al’umma, Hajiya Fa’ika M. Ahmed, ta bayyana haka a lokacin da take mayar da martani kan kudurin dokar da majalisar ta amince da shi a karkashin jagorancin kakakin majalisar, Nasiru Ma’azu Magarya.
Takardar godiyar ta samu sa hannun babban sakatare na ma’aikatar jin kai da kula da bala’o’i da ci gaban jama’a Bashir Kabir Ahmad a Gusau babban birnin jihar.
Hajiya Ahmed ta ci gaba da cewa, ‘yan majalisar dokokin da aka gudanar da su gabanin zartar da kudurin dokar ya nuna cewa majalisar a shirye take ta kara kaimi da himma da kokarin Gwamna Bello Muhammad wajen rage wahalhalun da marasa galihu ke fama dasu a fadin jihar.
Ta ce shirye-shiryen kare lafiyar jama’a sun shafi bangarori daban-daban, wanda ya hada da dukkan MDAs na bangaren zamantakewa kamar yadda ma’aikatar kula da jin kai, kula da bala’o’i, da ci gaban zamantakewa ta tsara.