Gwamnonin jihohi 36 sun gayyaci Gwamnan Babban Bankin Najeriya CBN, Mista Godwin Emiefele, don wani taron tattaunawa a ranar Alhamis kan batutuwan da suka shafi sabbin takardun kudin Naira da babban bankin ya bullo da shi.
Shugaban, yada labarai da hulda da jama’a, sakataren kungiyar gwamnonin Najeriya NFG, Abdulrazak Bello-Barkindo, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata a Abuja.
KARANTA WANNAN LABARIN: Hukumar Kwastam Ta Kama Kayan ‘Yan Sanda Da Na Sojoji Makonni Kafin Zuwan Zaben 2023
Bello-Barkindo ya ce taron, bisa ga gayyatar da shugaban NGF, Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sakkwato ya yi wa Emiefele, zai fara ne da karfe 9.
“Da yake bayar da goron gayyata, Darakta Janar na Kungiyar Gwamnonin Najeriya, Mista Asishana Bayo Okauru, ta ce ajandar tana kan manufofin CBN na sake fasalin kudin Naira,” in ji Bello-Barkindo.
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa babban bankin na CBN ya sanar da matakin farko na bankin Apex na sake fasalin kudin Naira a ranar 26 ga watan Oktoba, 2022, yayin da ya kuma sanya ranar 31 ga watan Janairu, 2023, a matsayin wa’adin tsohon takardar kudin.
Bello-Barkindo ya bayyana cewa ajandar taron tattaunawa mai taken “Tattalin Arziki da Tsaro na sake fasalin tsarin Naira da kuma cire kudi.”
“Tattaunawar ta yi alƙawarin samar da haɗin kai da tattaunawa tsakanin masu ruwa da tsaki daban-daban, ciki har da gwamnatoci da ƙungiyoyin jama’a don fito da hanyar warware matsalar da ta daɗe.”NAN
A wani labarin kuma, Buhari Ya Rubutawa Majalissar Dattawa Wasika, Ya Nemi Sake Nada Kwamishinonin ICPC
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya rubutawa majalisar dattijai wasikar neman amincewa da sake nada wasu mambobi bakwai na hukumar yaki da rashawa mai zaman kanta.
Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan, ya karanta wasikar tabbatar da kwamishinonin, mai kwanan wata, 3 ga watan Janairu, 2023 a zauren majalisar ranar Talata.