Wani mai wasan barkwanci ya caccaki ɗabi’ar nan ta duƙawa da mazaje ke yi domin neman samun amincewar macen da suke da muradin aure.
Ɗabi’ar duƙawar da mazaje ke yi dai na da aukuwa ne lokacin da mutum ya shirya neman yardar budurwar da yake soyayya da ita da ta yarje masa ya aure ta.
KU KARANTA KUMA: Wata budurwa ta nuna tagomashin da ta samu bayan ta kwashe kuɗin karatunta ta fara kasuwanci da su
A cewar mai wasan barkwancin mai suna Ahmed Isah, wannan ba al’adar mutanen nahiyar Afrika bane.
A cewar sa, duƙawa domin neman yardar mace wajen auren ta ya nuna cewa wanene wanda zai jagoranci akalar tarayyar da za su yi.
A cikin wani bidiyon da shafin Linda Ikeji ya sanya a manhajar Instagram, mai wasan barkwanci yayi nuni da cewa wannan ɗabi’ar ba tamu bace mutanen nahiyar Afrika.
A dalilin sa kuwa shine namiji ne yake auren mace ba mace bace take auren namiji.
A yanzu dai wannan ɗabi’ar ta zama ruwan dare a wajen ƴan Afrika inda mazaje ke duƙawa domin neman yardar masoyan su mata idan suka shirya neman auren su.
Shugaba Buhari Ya Karbi Lambar Yabo Ta Zaman Lafiya a Afirka
A wani labarin na daban kuma, shugaba Buhari ya samu muhimmiyar lambar yabo ta zaman lafiya a nahiyar Afrika.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Talata a birnin Nouakchott na Jamhuriyar Musulunci ta Mauritaniya, ya bukaci shugabanni da su ba da fifiko kan ci gaban matasa, tare da taka tsan-tsan da ra’ayoyin da za su dace wajen inganta sana’o’i, tare da hana zaman banza.
Da yake jawabi a taron zaman lafiya na Afirka, a shekarar 2023, shugaban ya ce rashin zaman lafiya da matasa ke yi da kuma rashin sanya baki wajen tattaunawa kan batutuwan da suka shafi rayuwarsu da kuma makomarsu na nuni da alhakin da nahiyar ke fuskanta, musamman a fannin tsattsauran ra’ayi.