Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, tare da takwaransa na Kaduna, Malam Nasiru Ahmed El-Rufai sun kaddamar da rukunin gidaje 500.
Kaddamar da rukunin ginin gidaje 550 wani yunkuri ne na samar da gidaje masu araha ga al’ummar Jihar
Inuwa yace Matakin zai jawo hanakalin masu zuba jari ciki da wajen jihar…
DUBA WANNAN: Domin Samun Labarai
Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, tare da takwaransa na Kaduna, Malam Nasiru Ahmed El-Rufai, a ranar Asabar din da ta gabata, sun gudanar da bikin kaddamar da wani sabon salon rukin gidaje da aka fi sani da Shongo Gardens Layout.
KARANTA WANNAN LABARIN: Sabbin Lambobin Ababen Hawa Na Taimawa Wasu Hukumomi Bin Diddigin Masu Laifuka – FRSC
Inuwa yace kaddamar da rukunin ginin gidaje 550 wani yunkuri na samar da gidaje masu araha ga al’ummar Jihar.
TRIBUNE ta rawaito cewa da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Inuwa Yahaya ya lura cewa, saboda kasancewarsa a shiyyar Arewa maso Gabas da kuma matsalar rashin tsaro da ake fama da ita a jihohin da ke makwabtaka da jihar Gombe ta samu karuwar jama’a da kuma karuwar girman garuruwanta.
Ya yi bayanin cewa wani bangare na samun sakamakon yawaitar ’yan gudun hijirar da kuma zama cikin birane, lamarin da ya ce ya kara matsin lamba kan abubuwan more rayuwa da ake da su tare da kara yawaitar bukatar gidaje da sauran ayyukan jin dadin jama’a.
A cewarsa, “Tun da aka kafa, mun fahimci cewa a kokarinmu na cimma burin SDGs na 11 na samar da dorewar al’umma da ci gaban birane, dole ne mu bullo da sabbin hanyoyin samar da gidaje masu araha da inganci ga jama’armu.
“A kan haka ne gwamnatinmu ta ga ya dace a kafa Gombe Geographic Information Systems GOGIS, tare da mayar da hukumar raya kasa ta jihar Gombe zuwa hukumar raya birane ta jihar Gombe GOSUPDA, domin tabbatar da ganin an cimma manufar sabunta birane tare da kawar da harkokin mulki.”
A cewar Gwamnan, tagwayen gidajen sun yi nuni da wani sabon salo na ci gaban ababen more rayuwa a jihar da kuma wani muhimmin mataki da zai tabbatar da ganin an aiwatar da ayyukan ci gaba na musamman wanda ke kunshe da kyakkyawar manufa ta gwamnatinsa na wani sabon salo da Gombe ta zamani.
“Wannan shimfidar za ta kasance irinta ta farko inda za a samar da muhimman ababen more rayuwa kamar tituna, ruwan sha, hanyoyin samar da wutar lantarki da sauran muhimman ayyuka da nufin samar da muhallin zama ga mazauna Gombe, tare da jawo hankalin masu zuba jari da masu ci gaba.” inji shi.
Sai dai Gwamnan ya yi gargadin cewa gwamnatin sa ba za ta lamunci duk wani aiki na zagon kasa, murdiya, ko yin katsalandan a cikin sabon tsarin ba, yana mai kira ga dukkan hukumomin da abin ya shafa da su tabbatar da bin ka’idojin ci gaba a yankin.
Takwaransa na Kaduna Nasir Elrufa’i ya yabawa Gwamna Inuwa bisa hangen nesa da yayi kamar yadda tsare-tsare na gwamnatinsa suka tabbatar da dawo da martabar al’ummar Jihar Gombe.
Gwamnan Kaduna ya ce, “Kamar yadda muke a Kaduna, an karkatar da shimfidu tare da karkatar da filaye, akwai sassaka a GRA kuma ba a yi wani karin shimfida ba, mutane suna yin gine-gine ba tare da bin ka’ida da sauransu ba.
“Akwai bukatar yin tanadi da tsare-tsare cikin gaggawa ga biranenmu da cibiyoyin biranen mu don samar da yanayi mai kyau ga yawan karuwar jama’a. Kuma haka Gwamna Inuwa yake yi a Gombe.
“Haka kuma yana ci gaba da ganin Gombe ta kasance mafi kyawun zabi ga masu zuba jari, na yi imanin cewa shi ya sa Gombe ta ci gaba da kasancewa a matsayinta na mafi kyawu a cikin saukin kasuwanci a kasar nan,” in ji shi.
A wani labarin kuma, Gwamnan APC Ya Bayyana Yadda Tinubu Ya Zama Zababben Shugaban Kasa
gwamnan jihar Filato, Simon Bako Lalong ya bayyana yadda Asiwaju Bola Tinubu ya samu nasarar lashe zaben shugaban kasa na 2023.
Lalong ya ce samu nasarar tasa ta biyo bayan mika mulki ga yankin Kudancin Najeriya da gwamnonin jihohin Arewacin Najeriya na APC suka yi.