Shugaban hukuma kiyaye hadura ta kasa Dauda Biu yace bullo da sabbin lambobin ababen hawa suna taimakawa wasu hukumomi.
Biu yace sabbin lambobin suna taimakawa wajen bin diddigin sawun masu aikata laifuka.
Sabbin lambobin ababen hawan sun taimaka wajen kwato motoci 383 da aka sace a cikin shekaru goma da suka gabata…
DUBA WANNAN: Domin Samun Labarai
Shugaban hukumar kiyaye hadura ta kasa, Dauda Biu, ya ce bullo da sabbin lambobin mota ya taimakawa wasu hukumomi irin su ‘yan sanda, hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa da kuma hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta da sauran laifuka masu alaka wajen gano masu aikata laifuka.
KARANTA WANNAN LABARIN: Ku Daina Kai Wa Jami’an Mu da Motocin Aiki Hari – FRSC
Ya yi nuni da cewa, binciken da aka yi wajen samun sabbin lambobin ababen hawa ya sa hukumar ta FRSC ta samu kwakkwaran bayanai, wanda sauran hukumomin za su iya amfana da su.
Biu, a wata tattaunawa da ya yi da wakilinmu a kwanakin baya, ya yi nuni da cewa, sabbin lambobin sun taimaka wajen kwato motoci 383 da aka sace a cikin shekaru 10 da suka gabata.
Kazalika ya ce tun bayan da aka bullo da sabon tsarin lambobin ababen hawa a shekarar 2011, an samar da sama da miliyan 12 na lambobin motocin.
Ya ci gaba da cewa, “A bayanan da muka samu adadin lambobin da aka samar tun daga farko ya kai 12,018,646.
Sannan daga bayanan da muka samu, mun kwato motoci 383 da aka sace a cikin shekaru 10 da suka wuce daga 2013 zuwa 2022.
“Hatta ‘yan sanda, da hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, hukumar yaki da rashawa mai zaman kanta da sauran laifuka masu alaka, da sauran hukumomi da dama sun dogara da bayanan mu daga sabbin tsarin lambobin.”
Da aka tambaye shi adadin motocin da aka yi wa rajista a kasar nan a halin yanzu, ya ce, “Jimillar motocin da aka yi wa rajista da inganci sun kai 6,623,309. Adadin ya kebanta da motocin gwamnatin jihohi.”
Da yake bayar da karin haske kan matakin aiwatar da hakkin wadanda hadarin mota ya shafa, ya ce hukumar na kokarin ganin an hukunta masu abin hawa kan raunuka da mutuwar fasinjojin.
Ya kara da cewa, “Muna aiki don ganin yadda za mu bi masu hakkinsu. Ya kamata a biya wadanda abin ya shafa ko iyalansu diyya.
“Kamata ya yi a samar da wata hanya ta doka ta yadda za a hukunta masu abin hawa kan raunin da fasinjojin suka samu da kuma mutuwarsu.
“Muna aiki da kungiyar lauyoyin Najeriya. Mun yi aiki da wasu kamfanoni a baya amma muna so mu mai da shi al’amuran kasa kuma shi ya sa muke aiki da NBA.”
A halin da ake ciki, FRSC ta gargadi masu ababen hawa da su yi taka tsantsan yayin tuki a lokacin damina domin guje wa asarar rayuka da dukiyoyi.
Kakakin hukumar FRSC, Bisi Kazeem ne ya bayyana hakan a wata hira da yayi da jaridar Sunday PUNCH a kwanakin baya
A wani labarin kuma, Gwamnan APC Ya Bayyana Yadda Tinubu Ya Zama Zababben Shugaban Kasa
gwamnan jihar Filato, Simon Bako Lalong ya bayyana yadda Asiwaju Bola Tinubu ya samu nasarar lashe zaben shugaban kasa na 2023.
Lalong ya ce samu nasarar tasa ta biyo bayan mika mulki ga yankin Kudancin Najeriya da gwamnonin jihohin Arewacin Najeriya na APC suka yi.