Babban Sufeto Janar na ‘yan sanda, Usman Baba, ya bayar da umarnin tura kwamishinonin ‘yan sanda guda bakwai zuwa wasu rundunonin ‘yan sanda a jihohi da sassan kasar nan.
DIMOKURADIYYA ta tattaro cewa Kakakin rundunar, CSP Olumuyiwa Adejobi, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a a Abuja.
KARANTA KUMA Dole Ne A Daina Kona Ofisoshin Hukumar Zabe INEC
Ya ce tura jami’an ya biyo bayan kammala babban darasi na 44 a cibiyar nazarin manufofi da tsare-tsare ta kasa NIPSS da wasu manyan jami’ai suka yi.
Mista Adejobi ya ce sabbin kwamishinonin da aka tura su ne: Sadiq Abubakar, FCT; Frank Mba, shedkwatar rundunar sintiri ta kan iyaka da; Arungwa Udo, Sashen Kudi da Akanta, Ofishin Tsaro ta rundunar kwararru, shedkwatar Rundunar.
Ya ce sauran sun hada da Bardaru Lawal, babban bincike, rundunar ‘yan sanda da ke Kaduna da; Suleiman Yusuf, Admin, Bincike da Tsare-tsare,a shedkwatar rundunar.
Mista Adejobi ya ce Ebong Ebong, Admin DFA, shedkwatar rundunar da; Babaji Sunday, kwamandan ‘yan sanda College Maiduguri, za su fara aiki nan take.
Ya ce babban sufeton ya bukaci sabbin jami’an da aka nada da su taka rawar gani a fagen yaki da laifuka, hadin kan jama’a da kuma tsaro.
Mista Adejobi ya ce shugaban ‘yan sandan ya kuma bukaci goyon baya da hadin kai daga jama’a ga sabbin shugabannin ‘yan sanda domin su samu damar gudanar da aikinsu yadda ya kamata. NAN/DailyNigerian.
A Wani Labarin Kuma Ba Zan Yarda Ayi Min Kishiya Ba — Inji Wata Amarya Ta Fadawa Mijinta
Matar Yul Edochie ta farko, May Edochie, ta mayar da martani ga uzurin da mai gidanta ya bata na bukatar karin auren wata matar.
Sai dai matar ta sa ta yi bore ga bukatar tasa duk da uzurin da ya bata na yana da bukatar yin hakan.