Yan kwanaki kenan bayan bazuwar labarin wata ma’aikaciyar jinya da ta caccaka allura wa wata jaririya a asibitin koyarwa na Usman Danfodiyo dake Sokoto, asibitin ya bada umarnin dakatar da ita nan take.
Ma’aikaciyar jinyar ta ce ta yi wannan mummunar aika-aika ne da zummar ramuwar gayya kan abinda mahaifiyar jaririyar ta yi mata na maido da ita makaranta sakamakon kada ita a jarabawa wato Carry Over a turance.
Da yake jawabi wa manema labarai a birnin Sakkwaton Shehu, Babban Daraktan Lafiya na asibitin mai suna Dakta Anas Sabir ya ce ma’aikaciyar jinya da a yanzu haka take tsare a gidan gyaran tarbiya dake jihar, ya ce dakatarwar tata zai ci gaba ne har sai abinda bincike ya tabbatar.
Ya ce “Idan aka kama ta da laifi yo tilas ne mu kore ta daga aiki baki ɗaya, amma yanzu dakatarwar har sai baba ta gani ne”
Idan ba a mance ba dai makonni biyu da suka gabata ne aka zargi ma’aikaciyar da caccaka wa jaririyar allura jim kadan bayan zuwanta duniya wai da zummar daukar fansar abinda mahaifiyarta ta yi mata a Cibiyar Jami’ar Karatu daga gida inda nan ne mahaifiyar tata ke aiki.
Da take zantawa da manema labarai, mahaifiyar jaririyar mai suna Asma’u Ahmad Tijjani ta yi waiwaye cewa nas din ta sameta ana makonni biyu gabannin haihuwarta kan cewa tana da wani sirri da ita da take son tattaunawa.
Ta ce “Bayan na tashi kan mu yi magana, sai ta fara mun tambayoyi, shin yaushe ne ake sa ran zan sauka, sannan yaushe zan je asibiti kuma menene cikakken sunana?
“To ganin cewa babu wata alaƙa ta keke da keke da ta taba hadani da ita, ya sa na ƙi gaya mata duk wadannan abubuwa da ta tambaya” Cewar Asma’u.
To sai dai a cewar mahaifiyar jaririyar, ma’aikaciyar jinyar mai suna Folake Folasade ta nusar da ita kan cewa tana da muradin taimaka mata ne yayin hajihuwar tata, lamarin da ya sa ta saki jiki.
“Jim kadan bayan na sauka lafiya ne sai ta zo ta karbi jaririyar don nuna ta wa mai gidana, ganin cewa ban aminta da ita ba sai na ce wa wasu nas-nas da su bi ta amma ta yi kirmimis ta ce ba za a yi haka ba”
Ta kara da cewa “Bayan wasu yan mintoci sai gata ta dawo mun da jaririyar, dauke da jini shame-shame a fuskarta, hakan ya sa ni tusa ihu amma kafin a ankara a nemeta an rasa”
Yanzu haka dai an sallami wannan mahaifiya da jaririyar ta daga asibiti, amma abinda ya fi ɗaga wa likitoci da ita kanta Asma’u shine tabbacin ko shin jaririyar za ta iya gani ko a’a, lamarin da aka ce sai ta fara girma za a tabbatar da hakan.