Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya umarci Hafsoshin tsaron kasar nan da su bankado duk wasu masu hannu a aikin sace-sacen mutane da fashin da sauran harkokin ta’addanci a kasar.
Shugaba Buhari ya bada Wannan umarni me yayin ganawar shi da Hafsoshin tsaron gabannin tashin sa zuwa Birnin Landan din duba lafiyar shi.
Shugaba Buhari ya ja kunnen Hafsoshin tsaron da cewa babu wasu tsiraru da za a bar su suna tada hankalin al’umma don haka dole a yi maganin su.
Ya Kuma kara da cewa babu daga kafa kan dokar dakatar da harkar hakar ma’adinai a Jihar Zamfara da kuma haramta tashin jirage a sararin samaniyar Jihar.