Hukumar jin dadin Alhazai ta Kasa NAHCON ta bayyana cewa ma’aikatar aikin Hajji da Umrah ta kasar Saudiyya ta sanar da shirin gudanar da aikin hajjin shekarar 2023.
Shugaban kuma babban jami’in hukumar NAHCON, Alhaji Zikrullah Hassan ne ya bayyana hakan a wajen taron masu ruwa da tsaki na aikin Hajji na shekarar 2022, wanda aka gudanar a dakin taro na masallacin kasa, ranar Alhamis din nan a Abuja.
DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa Hassan ya bayyana cewa an shirya taron ne domin hada kan ma’aikatan aikin hajji a Najeriya domin yin nazari tare da duba aikin hajjin na 2022 tare da samar da mafita ga kaluban da aka fuskanta don inganta aikin.
KU KARANTA KUMA Sama Da Yan Najeriya 3600 Ne Zasu Rasa Halartar Aikin Hajjin Bana
“Hajjin 2023 ya kusanto, ya dace mu mai da hankali kan tsare-tsare masu kyau da kuma taka tsantsan tare da sanin cewa burinmu shi ne mu faranta wa Allah ta hanyar mahajjatanmu da suka ba da jari mai yawa da nufin bauta wa Ubangiji shi kasai.
“Ina mai farin cikin sanar da ku cewa, sabanin aikin Hajjin da ya gabata da aka fara shirye-shiryen a makare saboda rashin samun bayanai, Ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya ta sanar da mu cewa za a fara shirye-shiryen aikin Hajjin 2023 da wani taro ta hanyar sadarwa na allon gani ga ka da aka shirya a ranar 21 ga watan Disamba tsakanin NAHCOH da ma’aikatar,” inji shi.
Hassan ya bayyana cewa manufar tsarin Hajjin 2023 ita ce a kiyaye matsayin da ake da shi; “Wato gudanar da tsarin ceton Aikin Hajji daidai gwargwado tare da biyan kuɗaɗen da kuka saba yi, kamar yadda aka yi a lokacin aikin Hajjin bana.”
Shugaban Hukumar ta NAHCON ya yabawa shugabannin Hukumar jin dadin Alhazai a dukkan Jihohin da suka bayar da gudunmawa da kishin kasa wajen aiwatar da shirin ceton Mahajjita da kuma sauran masu ruwa da tsaki.”
Ya bayyana cewa za a karrama wasu jihohin da suka yi rawar gani a aikin hajjin 2022.
A Wani Labarin Kuma Zaben 2023: Na’urar BVAS Zata Zama A Shirye Kafin Watan Disamba – INEC
Dukkan Tsarin Tabbatar da Zabe na BVAS da ake buƙata don gudanar da babban zaɓe na 2023 zasu kasance a shirye kafin watan Disambar wannan shekarar.
Kwamishinan INEC na kasa kuma shugaban kwamitin wayar da kan masu kada kuri’a, Mista Festus Okoye ne ya bayar da wannan tabbacin a Abuja ranar Alhamis.