A Kalla Mutane Hamsin da takwas ne suka hallaka a wani yanki na Jamhuriyar Nijar dake Iyaka da Kasar Mali, Kamar yadda gwamnati ta bayyana.
Wasu ƴan bindiga ne dai suka buɗe wuta wa wasu matafiya dake kan hanyar su ta dawowa daga kasuwa a yankin Tilabéri.
Kawo yanzu dai babu wani ko wata Kungiya da ta ɗauki alhakin wannan hari, toh sai dai akwai yan tada kayar baya da suka ɓullo a Kasar ta Nijar iyakar ta da Mali da Burkina Faso, da Kuma iyakar dake Kudu Maso Gabashin Najeriya.
Kuma tuni Kasar ta ayyana zaman makoki na kwanaki uku daga yau Laraba.
Gwamnatin kasar ta kuma bukaci Jama’a da su tashi tsaye wajen ganin sun fatattaki harkar miyagun mutane dake kokarin gurgunta kasar.