• Haryanzu Ina Nan Daram a Jam’iyar PDP inji Dan Majalisa Mai wakiltar Anka da Talatar Mafara na jihar Zamfara.
• “Idan na fita daga jam’iyar PDP kaman nayi mata butulci kenan ai” Inji shi.
• Jam’iyar PDP ta na Nan tana wasu shirye-shirye domin cigaban al’uma.
Dan majalissa Mai wakiltar Kananan hukumomin Anka da Talatar Mafara na jihar Zamfara, a majalissar wakilan kasar nan Honarabul Kabiru Classic, ya tabbatar da cewa, bagudu ba ja da baya, dangane da zaman sa a jam’iyar adawa ta PDP, duk da ficewar Gwamnan jihar Muhammad Bello Matawalle daga jam’iyar ta PDP zuwa APC.
Dan majalissar ya yi wannan batu ne a zantawar sa ta wayar salula, da gidan talbijin din yanar gizo wato Thunder Bluwers dake jihar Zamfara. Inda ya ce “Babu dalilin da zai sa, na bar jam’iyar PDP na koma Jam’iyar APC ” inji shi.
Ya kara da cewa, “Kowa ya sana’ata ada waka ce, Amma na dena, sabida banson cin Amana, hakan yasa na bar sana’ar na koma siyasa kuma Allah ya bani nasaran cin zabe a karkashin jam’iyar PDP, don haka banga dalilin da zai sa na bar jam’iyar ba, domin idan nayi hakan, yin butulci ne ga abun da jam’iyar tai mun abaya” inji Dan majalissar.
Kazalika ya ce, Canza shekar da sauran takwarorin sa guda shida su kayi, da sanatoci guda 3 na jihar, bazai sa ya razana ba, kuma shi da Allah ya dogara akan dukkan lamurorin shi.
KARANTA WANNAN LABARIN: Alkalin Alkalai ya ja kunnen Sabin Alkalan da ya nada
Ya kuma ce, ” Nayi imanin cewa Allah zai taimakeni, kuma da Allah ya jarab ce ni akan nayi karya, gwamma ya jarab ceni akan na yi gaskiya” a cewar sa.
A karshe ya yi kira ga magoya bayan shi da su cigaba da Maramashi baya, da kuma jam’iyar PDP, inda ya ce, “Jam’iyar ta na wasu shirye shirye na musamman, domin cigaban al’uma.