•Alkalin Alkalai ya rantsar da Alkalai goma sha takwas a kutunan dauka-ka Kara.
• Ya rantsar da su ne a Yau litinin a dakin taro na Kotun Kolin dake Abuja.
• Ya bukaci Alkalan da su guji karban cin hanci da rashawa.
Alkalin Alkalan kasar nan Ibrahim Muhammad ya gargadi Sabin Alkalan da ya rantsar da su a yau, da su guji karban cin hanci da rashawa a daukaci rayuwar su.
Muhammad ya gargade su ne lokacin da ya ke rantsar da sabbin alkalan guda 18 na Kotun dauka-ka Kara.
KARANTA WANNAN LABARIN: Wani ya kashe matar shi sabida Naira 2,000 a jihar Edo
Bikin rantsar da sabbin Alkalan ya gudana ne, a dakin taro na Kotun Kolin da ke Abuja, wanda aka rantsar da su, akwai Maza 15 da kuma Mata 3.
A karshe ya ta ya su murnan samun wannan matsayin, inda kuma ya yi kiran da su tabbatar da yin adalci kamar yadda doka ta tana, lokacin da suke gudanar da aiki.
Comments 1