Kungiyar Gwamnonin Nijeriya ta ce farmakin da gungun maharan da ake kyautata zaton mayakan Boko Haram ne suka kaiwa tawagar gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum a garin Baga, alama ce dake nuna cewar su kansu gwamnoni ba su tsira daga barazanar kungiyar ta Boko Haram ba.
Shugaban kungiyar gwamnonin Nijeriya, kuma gwamnan jihar Ekiti Kayode Fayemi ne ya fitar da sanarwar hadin gwiwar ga manema labarai, bayan taron da suka yi a ranar Litinin a Abuja.
Taron gwamnonin da ya maida hankali kan sha’anin tsaro, ya koka kan yadda lamurra ke kara tabarbarewa a sassan Najeriya, duk da kokarin gwamnati na kawo karshen matsalar.