Wani bincike da aka gudanar ya tabbatar da cewa motocin da yan kungiyar Inyamurai ta IPOB suka yi amfani da su wajen kai hari wa yan sanda a jihar Imo a yau na sata ne.
Yayin harin dai kamar yadda rahotanni suka bayyana, an hallaka ƴaƴan Ƙungiyar a kalla takwas yayin wata musayar wuta da aka shafe sa’o’i ana yi tsakanin su da yan sanda.
Majiyoyi da dama sun shaida cewa, yan ta’addan IPOB din sun kutsa yankin Orie Akokwa dake Ideato na birni Owerri inda suka yi kwacen motoci ciki har da Kira Range Rover SUV da Toyota Mini Bus gami da Hulux guda.
To sai dai bayan da suka farmaki rundunar yan sanda ta Orlu Division dake birnin na Owerri ne, daga bisani hakar su ta gaza cimma ruwa inda jami’an tsaro sum fatattake tare da nasarar kwace motocin.