By Abbas Yakubu Yaura
‘Yan ta’addan da ake kyautata zaton ‘yan Boko Haram ne da suka kai harin bam a jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna tare da sace fasinjoji da dama sun sako wata fasinja mai ciki abar tausayi.
A wani faifan bidiyo na musamman da jaridar DAILY NIGERIAN ta samu, matar (an sakaya sunanta) ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta tattauna da ‘yan ta’addan domin ceto rayukan wasu da ke tare da su.
Ta ce wadanda suka yi garkuwa da su sun kula da su tare da ciyar da su abinci da magunguna.
Majiyar tsaro ta shaidawa DAILY NIGERIAN cewa ba a biya kudin fansa ba kafin a sako ta.
Majiyar ta kuma yi watsi da rahotannin kafafen yada labarai na cewa mace daya ta haihu a hannun ‘yan ta’addan.
A ranar 28 ga watan Maris, ‘yan ta’addar sun dasa ababen fashewa a kan titin jirgin tare da samun nasarar hana jirgin motsawa.
Akalla fasinjoji takwas ne suka mutu a harin, yayin da aka yi garkuwa da wasu 168 ko kuma aka bayyana bacewarsu.
A ranar 6 ga watan Afrilu, ‘yan ta’addan sun sako manajan Daraktan Bankin noma, Alwan Hassan, bayan sun biya kudin fansa naira miliyan 100.