By Abbas Yakubu Yaura
Wasu ‘yan bindiga da suka yi garkuwa da jami’in dan sanda a jihar Zamfara, mai suna Sagir Hamidu, a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja a ranar Lahadin da ta gabata, sun bukaci Naira miliyan 200 a matsayin kudin fansa domin su sake shi.
‘Yan bindigar sun kuma bayar da wa’adin sa’o’i 6 ga iyalan dan sandan da su tara Naiara miliyan 200 don sakin wanda aka sace.
’Yan bindigar sun fusata ne a lokacin da ‘yan uwan sa suka roki cewa zasu iya biyan Naira miliyan biyu kacal. ‘Yan bindigar sun nuna bacin ransu tare da baiwa iyalan wa’adin sa’o’i 6, su biya kudin fansa Naira miliyan 200.”Masu garkuwan sun ci gaba da cewa, “Idan kuka sake ambatar Naira miliyan biyu, ko dai mu harbe shi har lahira ko kuma mu yanka shi.
Sun yi ikirarin cewa suna shirin yin kaura zuwa wani wurin daban saboda ba za su iya kiran waya ba kuma za su tafi da wanda suka sace.