A yau Litinin ne gwamnatin jihar Osun ta bayyana cewa za’a gudanar da zaman makoki na kwanaki uku a fadin jihar domin nuna takaici da jajantawa al’ummar jihar Ondo dangane da harin ta’addancin da aka kai a karshen makon da ya gabata, wanda ya yi sanadin rasa rayuka da jikkata wasu masu ibada.
Kwanaki uku na zaman makoki, a cewar wata sanarwa mai dauke da sa hannun kwamishinan yada labarai na jihar Funke Egbemode, zata fara ne daga ranar Litinin 13 ga watan Yuni; zuwa Laraba 15 ga watan Yuni shekarar.
A yayin zaman makokin, sanarwar ta kara da cewa, za a ayi kasa-kasa da dukkan tutoci a duk fadin jihar, kuma ana sa ran ‘yan jihar za su gudanar da harkokinsu cikin natsuwa domin girmama rayukan da ba su ji ba ba su gani ba, wadanda harin ya rutsa da su.
Yayin da take jajantawa wadanda harin ya rutsa da su da iyalansu na harin da aka kai a ranar Lahadi, 5 ga watan Yuni, 2022 a cocin Saint Francis Xavier Catholic Church dake garin Owo.na jihar Ondo, gwamnatin jihar Osun ta yi addu’ar samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata da ke ci gaba da jinya.
Idan za’a iya tunawa majiyar Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa gwamnan jihar Osun, Adegboyega Oyetola a ranar Lahadi, 12 ga watan Yuni, 2022, ya kai wa takwaransa na jihar Ondo, Rotimi Akeredolu ziyarar jaje a Akure dangane da lamarin.
A yayin ziyarar, Oyetola ya yi alkawarin yin aiki tare da sauran gwamnonin Kudu maso Yamma don karfafa rundunar tsaron yankin kudu maso yamma da kuma rundunar Amotekun domin samun cikakken tsaro a yankin.