A gasar ajin ƙwararru ta nahiyar turai da aka fafata a daren jiya da muma yammacin jiya, mai jagorantar ‘yan wasan na Tottenham wato Harry Kane ya jefa ƙwallaye guda 200.
Ya jefa cikason ƙwallo ta 200 dai dai daga wasanni guda 300 daya fafatawa Tottenham kuma ya jefa ƙwallon a kakar wasa daban-daban kuma a gasa faban-daban.
Kane dai ya kwashe shekaru da dama a ƙungiyar domin kuwa tun a shekarar 2009 yaje Tottenham kuma ayanzu haka a tarihin ‘yan wasan da suka fi jefa ƙwallaye a ƙungiyar, wato mutane 3 kenan harda Harry Kane a ciki.
Haka zalika a kakar wasa ta bana ana hasashen Tottenham na daga cikin kefin kungiyoyin kwallon kafan da ake ganin zasu iya lashe gasar ajin Firimiya ta Ingila duba da yadda Mourinho ya shirya tsaf.