Rahotanni sun bayyana cewa wasu Likitoci daga Jami’ar Toledo dake kasar Amurka sun gargadi mutane da su guji amfani da wayar tarho a cikin rana da duhu domin hasken na iya makantar da mutum. Shugaban Likitocin Ajith Karunarath ne ya bayyana haka inda ya kara da cewa an gano hakan ne bayan wani bincike na musamman da suka gudanar.
A cewarsa binciken da suka gudanar ya nuna cewa hasken dake fitowa daga waya da ake kira ‘Blue Light’ na iya kashe jijiyoyin da suke taimaka wa ido wurin ganin haske da sauran abubuwa da ake kira ‘Photoreceptors’ da turanci.
Karunarathne ya ce binciken ya kuma kara nuna musu cewa hasken na daya daga cikin abubuwan dake sa mutane a kasar Amurka kamuwa da cutar makanta.
A karshe ya ce domin guje wa irin haka ne suke kira ga mutane da su rika amfani da tabarau ko kuma maganin da zai taimaka wajen rage karfin hasken waya domin kada ya yiwa idanu illa.