Hukumar kiyaye hatsura ta kasa, FRSC reshen Osun a ranar Laraba ta bayyana cewa akalla mutum biyar ne suka tsallake mutuwa sakamakon hatsarin da ya rutsa da su a titin Ipetu-Ijesa-Akure.
Kwamandar FRSC reshen Osun, Kudirat Ibrahim, ita ce ta tabbatar da hakan a cikin sanarwar da Kakakin Hukumar Agnes Ogungbemi ta fitar a garin Osogbo.
Ibrahim ta ce mutum biyar din sun hada da maza biyu da mata uku, inda jami’an FRSC din suka ceto shi cikin motarsu kirar Mistubushi mai lamba APR 854 XA da ta rasa burkinta.