Hukumar Hisbah ta jihar Jigawa ta ce ta kama wasu mutane 47 da ake zargi da hannu a cikin ayyukan lalata da mata 16 a jihar.
Kwamandan Hisbah a jihar, Malam Ibrahim Dahiru, ya tabbatar da kamen a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya, ranar Laraba a Dutse.
Dahiru ya ce an kama wadanda ake zargin da suka hada da 16 da ake zargin masu yin lalata da karuwai ne, biyo bayan wasu hare-hare da aka kai a gidajen barasa da gidajen karuwai da sauran wurare a kananan hukumomi 11 na jihar.
Ya ce a farmakin da aka kai tsakanin 13 ga watan Oktoba zuwa 27 ga watan Oktoba, an kwace wasu kwalaben barasa iri-iri har guda 745.
KARANTA WANNNAN LABARIN: An Kama Mutane 4 da Ake Zargin Masu Garkuwa da mutane ne a jihar Sokoto
Ya Kuma kara da cewa, an kama wadanda ake zargin ne, ko dai bisa zargin shan giya, da goyon bayan masu yin lalata, da kuma sauran ayyukan lalata.
Kazalika ya Kuma ce, an mika wadanda ake zargin ga ‘yan sanda domin daukar matakin daya dace.
A cewarsa, an haramta shan barasa a jihar, sannan ya jaddada kudurin hukumar na ci gaba da yaki da duk wani nau’in lalata.