Asiwaju Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC mai mulki, ya karbi bakoncin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da wakilan kungiyar ECOWAS masu sa ido kan zabe a gidansa da ke Abuja ranar Talata, Daily Trust ta rawaito.
Tsohon shugaban Ghana, John Mahama, yana cikin tawagar ECOWAS da ta ziyarci Tinubu.
KARANTA WANNAN LABARIN: PDP Tayi Watsi Da Sakamakon Zaben 2023 a Jihar Borno
JARIDAR DIMOKURADIYYA ta rawaito cewa Mahama da Jonathan sun shugabanci kasashensu a lokaci guda kuma dukkansu sun sha kaye a neman sake zabensu a zagaye na gaba.
Tinubu, wanda ke kan gaba a sakamakon zaben shugaban kasar Najeriya ya yi murmushi yayin da ya tarbi bakinsa.
A wani labarin kuma, Buhari Ya Sake Nada Shugaban Hukumar Kare Hakkin Bil’adama Ta Kasa
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya rubutawa majalisar dattawa wasika ta tabbatar da Anthony Ojukwu, domin sake nada shi a matsayin babban sakataren hukumar kare hakkin bil’adama ta kasa.
A cewar wasikar da shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya karanta a zauren majalisar a ranar Talata, sake nadin na shekara biyar ne kuma zai kasance wa’adin karshe na Ojuku a kan mukamin.
Wasikar ta ce, “A bisa tanadin sashe na 7(2) na dokar hukumar kare hakkin bil’adama ta kasa, na shekarar 2010, na rubuta wasika zuwa ga majalisar dattawa domin ta tabbatar da nadin Mista Anthony Ojukwu, SAN.domin sake nada shi a matsayin Babban Sakatare na Hukumar Kare Hakkokin Dan Adam ta Kasa, na wa’adin karshe na shekaru 5.
“Yayin da nake fata Majalisar Dattawa za ta yi nazari tare da tabbatar da nadin kamar yadda aka saba a cikin gaggawa. Da fatan za a amince da irin tabbacin da Shugaban Majalisar Dattawan ya ba ni mafi girman la’akari da ni.”
Haka kuma, a wata wasika mai dauke da kwanan wata 1 ga watan Fabrairu, 2023, shugaban ya kuma nemi a tabbatar da nadin Hon. Mai shari’a Stanley Lawal, a matsayin shugaban kotun daukaka kara ta Kwastomari dake Abuja.