By Abbas Yakubu Yaura
Hukumar ba da ilmin bai daya ta jihar Bauchi BASUBEB ta mayar da yara 153,398 da ba sa zuwa makaranta ajujuwa a karkashin shirin (BESDA) dake kananan hukumomi 16 cikin 20 na jihar.
Shugaban SUBEB, Dakta Abubakar Sheikh Dahiru ya bayyana haka a lokacin daya bayyana buda manufar BESDA a fannin ilimin Almajiri a jihar.
Yace BESDA shiri ne na Bankin Duniya tare da hadin gwiwar gwamnatin tarayya da na jiha da nufin mayar da yaran da ba sa zuwa makaranta ajujuwa.
Sannan ya ce a kashin farko na atisayen da aka gudanar a shekarar da ta gabata, an mayar da dalibai 94,000 zuwa makaranta a kananan hukumomi tara kuma a bana an kara kananan hukumomi bakwai, wanda ya kai adadin zuwa kananan hukumomi 16 cikin 20 dake jihar.
Ya ce shirin yana kula da jin dadin daliban ta hanyar samar musu da yanayi mai kyau na koyo.
“Muna ba da duk kayan koyo da koyarwa, a gare su, muna samar da ruwa, bayan gida, sabulu, yunifom, nakasassu don saukaka jigilar su zuwa makaranta kuma muna samar da bukatu na musamman ga daliban, da sauransu.”
Ya kuma yi kira ga iyaye, al’umma da malaman addini dasu marawa gwamnati baya a kokarinta na ganin ilimi ya kai ga kofar al’ummarsu.
A jawabansu daban daban, masu kididdigar da shugabannin gargajiya dana al’umma sun godewa SUBEB bisa shirya taron horaswa da wayar da kan jama’a da tayi.