Hukumar CCB Ta Fara Binciken Kaddarorin Masu Rike Ofishin Siyasa
Hukumar da ke kula da Halayya (CCB) ta fara tantance dukiyar masu riƙe da muƙaman siyasa da kadarori na manyan jami’an Gwamnati a wani Yunƙuri na yaƙi da cin hanci da rashawa da aka sake farfadowa a ƙasar nan.
Shugaban riƙo na hukumar, Murtala Aliyu Kankia ya bayyana haka a lokacin da yake duba aikin tantancewar da ake yi a ranar Litinin a Jihar Katsina.
Ya ce atisayen binciken zai shafi manyan jami’an Gwamnati da Ma’aikatan Gwamnati da suka haɗa da Sakatarorin dindindin, da daraktoci da sauran manyan Jami’an Gwamnati.
“Na yi wa Gwamna Dikko Radda bayanin dalilin da ya sa muka zo Katsina, inda shima muka samu yana da kishin yaƙi da cin hanci da rashawa,” inji shi.
A cewarsa atisayen na da nufin gano sahihancin kadarorin da masu rike da mukaman siyasa da sauran manyan ma’aikatan Gwamnati suka mallaka a lokacin da suke kan karagar mulki.
KARANTA WANNAN LABARIN:Wata Ƙungiya mai zaman kanta ta buƙaci FG da ta sanya ilimin zaman lafiya a cikin darussan karatu a Najeriya
Hakan ya ce zai ƙara wa yaƙi da cin hanci da rashawa da Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ke yi, inda ya ƙara da cewa bayan kammala atisayen Jami’anta za su je filin domin tantance kadarorin da jami’an suka bayyana.
Kun san wasu mutane suna da dabi’ar shela na jiran tsammani har ma da rashin bayyana kadarorin su.
Don gano waɗannan abubuwa guda uku za mu je filin don gano inda wani da aka bayyana ko ake tsammanin yana da wani abun da ya bayyana a matsayin dukiyar shi domin tantance sahihancin shi.
Duk waɗanda laifuffuka ne. Kuma duk Mutumin da aka samu da laifin, to za a tura shi zuwa kotun CCB don hukunta shi.
Hukuncin shine, ko dai ya mayar da kadarorin, ko a hana shi riƙe mukamin Gwamnati na tsawon shekaru 10, ko kuma a nemi ya bar ofishin da yake ciki a lokacin.
Muna kan hanya muna yin hakan ne domin amfanin kasa da al’ummar mu,” inji shi.