Rundunar Ƴan Sandan Jihar Legas ta sake ƙwace baburan Okada 355
Rundunar Ƴan sandan Jihar Legas ta ce ta kama wasu babura na ƴan kasuwa masu haya guda 355 a wani samame suka kai da ya ɗauki kimanin sa’o’i biyar a ranar Litinin.
Jami’in hulɗa da Jama’a na Hukumar Mista Gbadeyan Abdulraheem ya tabbatar da kamun a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa tun a ranar 14 ga watan Janairu ne rundunar ta sanar da kwace babura 344 daga sassa daban-daban na Jihar cikin kwanaki bakwai.
Abdulraheem ya ce aikin na da wahala saboda yanayin da aka gudanar da shi da kuma rashin jituwar masu babura.
“Nasarar da muka samu a yau ɗaya ce daga cikin nau’ikan manyan nasarorin da muke samu, ta la’akari da Baburan da muka kama a wannan ran gadin.
KARANTA NAN:Ana zargin wani Kwamishina da amfani da Digiri Ɗan Cotonou
Mun ziyarci Alakija da Abule makonnin da suka gabata, amma sai da muka sake ziyartan wurin, har da ma kasuwar baje koli da ke kan babbar hanya Badagry.
Mun sanar da wannan sakamakon ne domin aikewa da kwakkwaran saƙo zuwa ga waɗannan mahaya okada cewa za mu ɗauki matakin da ba za su iya jurewa ban
Hukumar ta zo tsaf domin gudanar da aikin, inda ta cika dukkanin manyan motoci bakwai cike da Baburan da aka kwace a lokacin samamen.
Ya tabbatar ga waɗannan ƴan okadan cewa babu wurin zama a babban birni kamar Legas, shi ya sa muka ci gaba da kai musu samame ba ƙauƙautawa lokaci bayan lokaci, har sai da suka gudu suka chanja wuri,” inji shi.
Abdulraheem ya ce hukumar za ta gudanar da ayyuka masu tsauri tare da fadada shi zuwa kowane lungu da saƙo na Jihar har sai an samu nasara a yakin da ake yi da masu babura.
A wani labarin kuma:Hukumar CCB Ta Fara Binciken Kaddarorin Masu Rike Ofishin Siyasa
CCB Ta Fara Binciken Kaddarorin Masu Rike Ofishin Siyasa
Hukumar da ke kula da Halayya (CCB) ta fara tantance dukiyar masu riƙe da muƙaman siyasa da kadarori na manyan jami’an Gwamnati a wani Yunƙuri na yaƙi da cin hanci da rashawa da aka sake farfadowa a ƙasar nan.