Muƙaddashin Kwanturola-Janar na Hukumar Kula da Shige da Fice ta Ƙasa Idris Jere ya bada umarnin ɗauke Jami’ai guda biyu da daga Filin Jirgin sama na Ƙasa da Ƙasa na Murtala Muhammad dake cikin Lagos.
An cire su daga wurin a dalilin rashin iya aiki da suka nuna, kamar yadda mai Magana da Yawun Hukumar Amos Akpu ya bayyana a cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Juma’a.
KARANTA WANNAN LABARIN: Rikici: Wani Lauya Ya Bukaci A Kama Matar Tsohon Gwamna Obiano Da Bianca
Wani amfani da shafin Twitter ya bada labarin yadda wata ƙaramar yarinya mai shekaru 14 da zata bar Ƙasar, tasha wulaƙanci a hannun Jami’an.
Akpu yace Hukumar NIS, ta hanyar Twitter, ta tuntuɓi yarinyar, inda ta bada tabbacin ɗaukar mataki.
Inda daganan muƙaddashin Shugaban Hukumar ya bada umarnin a duba Na’urar data ɗauki hoto, tare da duba abinda ya faru a wurin.
Tawagar da aka naɗa ta gudanar da bincike a Jirgin Sama na Lagos, Kemi Nandap ya Tabbatar da aikata laifin daga Jami’an.
Akpu ya bayyana cewar an kama su dumu-dumu da rashin iya aiki a lokacin da suke tantance matafiyan.
“An cire su daga Filin Jirgin sama, kuma a halin yanzu suna karɓar horo, kamar yadda Muƙaddashin Kwanturola-Janar ya buƙata.”
Jere yace mulkin sa bazai lamunci duk wani cin mutunci ba, inda yayi kira ga Al’umma da sukai rahoton irin waɗannan lamurran ga Hukumar.