Hukumar kula da harkokin ‘yan fansho ta PTAD, ta ce bayan nazari kan yan fansho a Nigeria, hukumar ta biya yan fansho Dubu Ashirin da Hudu kudin da yawansu ya kai Naira Biliyan Bakwai a fadin kasar nan.
Sakatariyar zartarwa ta hukumar PTAD, Dakta Chioma Ejikeme ce ta bayyana hakan a lokacin kaddamar da sabuwar manhajar yanar gizo gay an fanshon domin karba mai suna ‘’Ina raye’’ a taron masu ruwa da tsaki na yankin Arewa maso Yamma da aka gudanar a Kano.
Dokta Chioma Ejikeme ta ce makasudin taron masu ruwa da tsaki na kwanaki biyu shi ne sanar da masu ruwa da tsaki abubuwan da hukumar ta yi, da sanar da su ilimin da ya dace na yadda za a shiga cikin aikace-aikacen yanar gizon na Ina da rai, da kuma sauran matakan da zasu biyo baya.
Ta ce cutar ta Covid 19 ta jefa duk duniya cikin mummunan koma baya wanda ya haifar da durkushewar duk wasu ayyuka a duk duniya.
Ta kuma ce duk da kalubalen da PTAD ke fuskanta har yanzu tana ci gaba da biyan kudaden fansho na wata-wata ba tare da bata lokaci ba, tana magance korafe-korafe, da kuma kawar da basussukan da aka tara, da diyya ga iyalan wadanda suka mutu da sauran su.