By Abbas Yakubu Yaura
hukumar hana fasa kwauri ta Najeriya (NCS) tace ta kama buhunhuna 250 na tabar wiwi da kudinta ya haura naira miliyan 10.4m, wadanda ake zargin suna kan hanyar zuwa jihar Katsina domin kaiwa barayi su yin amfani da ita, kamar yadda sashin kula da ayyuka na tarayya (FOU) shiyya ta B, ta bayyana.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Kwanturolan sashin FOU na shiyya ta B dake Kaduna, A.B. Hamisu, yace sauran magungunan da sashin FOU suka kama sun hada da: fakitin Tramadol guda 75,582 da ake zargin kudin su sun haura naira miliyan 29.7m.inda kuma hakan yake inganta ayyukan ta’addanci da sauran nau’ikan munana laifuka.
Fakitin guda 1,582 na D5 wanda kudinsu ya kai Naira miliyan 12,720,011.68 wadanda suka kasance ba su da kyau, saboda yana iya tayar da laifuka, inda yace an kama su.”
Sannan an kama masu laifin ne a wani kauye mai suna Basari dake cikin garin Katsina, ind ya tabbatar da cewa kayan anyi musu irin shirin ’yan fashin saboda haramtaccen kayan yana kunshe da kyau.”
Muna kira ga jama’a da suke da bayanai kan irin wadannan haramtattun abubuwa da su mika wa jami’an tsaro domin daukar matakin gaggawa.”
“Duk wanda yake da bayanai akan irin wadannan to ya isar mana da shi. Duk bayanan da muka samu suna cikin sirri,” ya yi alkawari.