Hukumar Dake lura yadda ake kashe kudaden gwamnati ta kasa ta karrama gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje bisa yadda yadda ya ciri tuta wajen shugabanci, tare da bayyana shi a matsayin jajirtacce wajen gabatar da kasafi mai ma’ana, shugabanci nagari da kuma taka tsan-tsan wajen amfani da dukiyar al’umma.
Yayin ziyarar da shugaban hukumar na kasa Barrister Victor Muruako, ya kaiwa gwamnan a gidan gwamnatin Kano a yau, ya kuma sake karfafawa gwamnan gwiwa wajen cigaba da dorawa kan kyawawan manufofinsa wadanda zasu ciyar da jihar da kuma al’ummar ta gaba.
Barrister Victor ya kara da cewa sunzo jihar Kano ne domin gudanar d ataron karawa juna sani kan harkokin da suka shafi Kasafin kudi, da shugabanci na gari, tsawon kwanaki biyu, da aka shirya baiwa jami’an gwamnati dama wadanda basa karkashin gwamnati, sai kuma wasu daga cikin hukumomin gwamnatin tarayya dake yankin Arewa maso yamma.
A nasa bangaren gwamna Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya yabawa hukumar bisa zabar jihar Kano domin gudanar da wannan taron, tare da godea hukumar kan yadda take cigaba da habbaka bangaren daya shafi kasafin kudi