By Abbas Yakubu yaura
Hukumar hana fataucin bil’adama ta kasa (NAPTIP) tace sama da mutane 2100 ne aka gurfanar dasu a gaban kotu a shekarar 2020.
Ministar harkokin mata, Dame Pauline Tallen, ce ta bayyana hakan a ranar Juma’a a Abuja yayin gabatar da rahoton aiwatar da dokar ta’addanci ta VAPP ta shekarar 2015.
Bayanan da aka bayar daga rundunar ‘yan sandan Najeriyar ta kuma bayyana cewa, an samu hukunci guda 155 kan laifukan cin zarafin mata da maza a kasar.
Rahoton yace an samu karuwar cin zarafi mata a fadin kasar a tsakanin shekarar 2019 zuwa 2020 kuma akalla sama da mutane 14,970 da suka tsira sun sami taimako daga cibiyoyin tunkarar cin zarafi.
Dame Pauline Tallen tace yawan cin zarafi na jiki, tunani kan mata da yara a cikin ‘yan kwanakin nan na da matukar tayar da hankali da ban tsoro.
“Ga wata shari’ar da aka bayar, zan iya tabbatar muku cewa ba a bada rahoton wasu kararraki 10 ba. Lokaci ya yi da za mu karya tsarin al’adu tare da karfafa wa wadanda suka tsira damar yin magana tare da basu duk goyon bayan da suke bukata da kuma tabbatar da cewa an yi adalci,” inji ta.
Ministan ta yabawa hukumar da duk masu ruwa da tsaki wajen aiwatar da dokar VAPP ta shekarar 2015.
Kazalika tace, “Yakin jima’i da cin zarafin mata ba karamin tasiri ba ne.Don haka yana da kyau dukkan hukumomi su hada kai tare da dabarun da zasu kawo karshensa.”
A jawabinta na bude taron, Darakta-Janar na Hukumar NAPTIP, Dakta Fatima Waziri-Azi, tace hukumar zata ci gaba da hada kai da ‘yan uwanta wajen ganin wadanda suka tsira daga cin zarafin mata da maza za su samu tallafi da taimakon da suke bukata.
Sannan tace, “Muna kara kokarinmu ta hanyar yin amfani da sa’o’i 24 na duk wani tsari na hannaye kan duk wani lamari na cin zarafi da jima’i don tabbatar da cewa babu wanda ya fada cikin tarzoma.
“Kuma don haɓaka saurin mayar da martani ga dukkan lamuran, ana samun rukunin martani cikin gaggawa a ofishina, da Ofishin DG.”