Hukumar Hana sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi NDLEA ta yi ram da hodar ibili da Kuma ganyen wiwi a filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano da Kuma Murtala Muhammad dake Legas da kudin su ya kai Kimanin Naira Miliyan goma.
Kakakin Hukumar ta Kasa Femi Babafemi ya ce a yayin wata jarabawar Kamfanin Cargo ne da aka gudanar da a jihar Legas wani dan kasar Afirka ta Kudu ya gabatar da jirgi kirar kamfani Ethiopian Airline inda nan ne aka yi ido biyu da miyagun Kayayyyakin
Ya kara da cewa bayan da jami’an filin jirgin saman suka zurfafa bincike ne dai sai fa suka fahimci cewa akwai wata tabara da ake shirin yi, inda aka boye miyagun Kayayyyakin cikin wata jar jaka da ake kira Ghana-must-go.
A wani labarin makamancin wannan a Jihar Kano Jam’ian NDLEA din sun chakfe wasu kwayoyi da aka yi harin birnin Manchester da su dake Kasar Birtaniya.
Tuni dai aka tura samfurin kwayoyin izuwa dakin gwaje-gwaje don tabbatar da ya al’amarin yake.
Kana a cewar Kwamandar Hukumar a Jihar Legas, za a ci gaba da gudanar da bincike ko za a sake yin arangama da wasu muggan mutane dake safarar miyagun Kayayyyaki.