Hukumar bada agajin gaggawa ta NEMA a ranar Laraba ta karbi ‘yan Najeriya 159 da suka fake a kasar Libya.
Sun sauka a filin jirgin saman Murtala Muhammed (MMIA) da ke Legas.
Darakta Janar na Hukumar NEMA, Habib Mustapha, wanda Mukaddashin Kodinetan Ofishin Yankin Legas, Ibrahim Farinloye ya wakilta shine ya tabbatar da hakan ga Kamfanin Dillancin labarai na kasa NAN.
Yan Najeriya sun isa tashar Cargo Wing na MMIA da misalin karfe 7.10 na safe. A jirgin sama na Al Buraq Airline mai lamba 5A-DMG.
Sun dawo ne tare da tallafin Hukumar Kula da Hijira ta Duniya (IOM) ta hanyar shirin mayar da marasa galihu dake zaune a kasashen ketare gidajensu.
Wadanda aka dawo da su sun hada da maza 67, mata 80, Yara maza shida da Yara mata hudu, tare da jarirai biyu (namiji daya da mace daya).
“Ya zama al’ada a rayuwa don gwagwarmaya don inganta rayuwa amma a cikin gwagwarmaya, dole ne mu guji jefa rayuwarmu cikin haɗari.” Inji shi
“A duniya babu inda ‘yan kasar ba za su yi yunƙurin samun rayuwa mai kyau cikin ƙarancin albarkatun da ake da su a ƙasar ba.”
“Najeriya na da kyakkyawar baiwa fiye da yawancin kasashen da matasan Najeriya ke balaguro zuwa neman wuraren sana’a da ba a nan kasar ba,” in ji shi.
Shugaban NEMA ya bukaci ‘yan kasar nan da su duba cikin gida su yi amfani da damammaki marasa adadi da Najeriya ke da shi.
Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS), Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira, Hukumar Kula da Jiragen Sama ta Tarayya (FAAN) da ‘yan sanda su ma sun karbi mutanen da aka dawo da su.