By Abbas Yakubu Yaura
Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa a ranar Larabar ta karbi ‘yan Najeriya 95 da suka makale daga kasar Libya a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Legas.
Habib Mustapha, Darakta Janar na NEMA wanda ya samu wakilcin mukaddashin kodinetan ofishin hukumar na Legas, Ibrahim Farinloye, ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya a Legas.
Farinloye yace ‘yan Najeriyan wadanda suka makale sun isa filin jirgin saman Murtala Muhammed ranar Talata da daddare da misalin karfe 20.18 na rana tare da kamfanin jirgin Al Buraq mai lamba UZ189/16/5A- DMG-MJI AD15:50 wanda ya kawo su gida.
Yace hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta duniya ce ta dawo da ‘yan gudun hijirar kasar ta hanyar shirin mayar da ‘yan gudun hijira na radin kansu ga matsugunan na asali da suka bar kasar don neman wuraren neman kudi a kasashen Turai daban-daban amma basu samu damar dawowa ba a lokacin da tafiyar tasu ta ci tura.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Farinloye ya kara cewa wadanda aka dawo dasu manya ne maza guda 60, da manyan mata 29, maza uku da mata daya, tare da jarirai biyu (daya namiji da mace).
Kazalika Farinloye yace, sashin kula da lafiya ta tashar jiragen ruwa na gwamnatin tarayya, da hukumar tserar da ‘yan gudun hijira, da kuma hukumar shige da fice ta Najeriya na daga cikin hukumomin gwamnati da suka tarbi mutanen da suka dawo a filin jirgin.