Wata tankar tanka da ta tashi da Wuta, da sanyin safiyar ranar Laraba ta halaka mutane biyar a hanyar Legas zuwa Ibadan.
Rahotanni sun ce wadanda lamarin ya rutsa da su sun kone kurmus a lokacin da lamarin ya faru a kusa da tashar Tunji Alegi da ke unguwar Kwakyama a Ogere na jihar Ogun.
Wata tankar mai dauke da man fetur ta fadi kan wata babbar motar dakon kaya, sannan ta zubar da kayan da ke cikinta sannan ta kama wuta, ta kone akalla mutane biyar.
Akalla motoci biyar ne kuma suka kone yayin fashewar.
Mai magana da yawun hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC), Florence Okpe, ta tabbatar da faruwar lamarin a ranar Laraba a Abeokuta.
KARANTA WANNAN LABARIN: Masu Garkuwa da mambobin NULGE 12 sun Bukaci Naira Milliyan 40
Okpe, wacce ita ce jami’iar kula da ilimantar da jama’a na FRSC, ta bayyana cewa tankar ta yi karo da wata babbar motar dakon kaya wanda hakan ne ya yi sanadin tashin gobara.
Ta dora laifin faruwar lamarin a kan ” Yin tuki daidai ba kuma tuki mai hatsari” daga bangaren direban tankar.
Okpe ta ce an zakulo gawarwakin wadanda abin ya rutsa da su daga cikin motocin da suka yi hatsarin kuma aka ajiye su a dakin ajiye gawa da ke Ipara a karamar hukumar Remo ta Arewa.
“kuma mutane biyar ne suka kone wadanda yanzu haka ba za’a iya gane su ba.”
“An zakulo su ne daga daya daga cikin manyan motocin da suka yi hatsari kuma an ajiye su a FOS Morgue Ipara.”
” Za muyi Karin bayani kan lamarin nan ba da jimawa ba, ”in ji ta.
Okpe ta yi nuni da cewa, an karkatar da ababen hawa a kan hanyar ne domin gujewa faruwan hakan a gaba, kamar yadda ta shawarci matafiya da su kwantar da hankula tare da bayar da hadin kai ga masu kula da ababen hawa.
Wakilin Jaridar Daily Trust ya ruwaito cewa, a daren Lahadi, mutane bakwai sun kone kurmus a hanyar Legas zuwa Ibadan.
A cewar hukumar ta FRSC, “jimillan mutane 10 ne suka shiga hatsarin”.