Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada wani jigon jam’iyyar APC, George Moghalu a matsayin sabon manajan Darakta na hukumar NIWA.
Jagoran kula da hakkokin hukumar, Tayo Fadile, shi ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya saki a Lokoja a ranar Laraba 2 ga watan Oktoba.
Hakazalika George Moghalu da tsohon Manajan Daraktan hukumar ta NIWA, Barista Danladi Ibrahim duk sun tabbatar da sabon shugabancin da aka samu.