By Abbas Yakubu Yaura
A ranar Juma’ar data gabata ne rundunar sojojin ruwa da masu yaki da barna da hukumar tsaro ta farin kaya ta Najeriya NSCDC a jihar Legas suka kama wasu da ake zargin barayin mai.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa wadanda aka kama din dai ana zarginsu da yunkurin safarar man fetur zuwa jamhuriyar Benin.
Wadanda ake zargin su biyar – Israel Oluwayemi mai shekaru 35, da Issa Quadri mai shekaru 49, sai Matthew Ayobami dan kimanin shekaru 29, da Altra Suwesa mai shekara 40 da kuma Adedoyin Elikena 52, dukkan su an kama su ne a bakin tekun Oniru.
An gano babban jirgin ruwa guda daya,dauke da ganguna mai 119 da kuma Premium Motor Spirit (PMS), ganguna 38 da babu komai a cikin sa, injinan fanfo guda biyu da injin mai karfin awo 60 a yayin aikin.
Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, Seun Abolurin ya fitar, tace an gudanar da aikin ne karkashin jagorancin shugaban sashin yaki da barna, Mataimakin Kwamanda na (ACC) Adegbayibi Adebayo, tare da goyon bayan Mataimakin Kwamanda Ayo Agoro.
Sanarwar ta kara da cewa: “Kwamandan, Eweka Okoro, ya umurci hukumar leken asirin ta fara gudanar da bincike a kan lamarin yayin da aka kai kayayyakin da aka kama zuwa rundunar jihar dake Alausa, Ikeja.
“An kuma tuntubi Hukumar Kula da Man Fetur ta Najeriya (NNPC) don fitar da kayayyakin yadda ya kamata saboda yanayin da yake dasu.”