MANCHESTER City na fuskantar hukunce-hukuncen da suka hada da tara da kuma cire maki zuwa kora daga gasar Premier yayin da gasar Premier ta tuhumi kulob din da saba ka’idojin kudi sama da 100 bayan wani bincike na tsawon shekaru hudu.
Mahukuntan Gasar Premier sun mika kungiyar ga wata hukuma mai zaman kanta bisa zargin karya doka tsakanin 2009 da 2018.
KU KARANTA: Karancin Sabbin Kudi Ya sa APC ta dage yakin neman zaben Tinubu
Ta kuma zargi City din da rashin bayar da hadin kai tun lokacin da aka fara binciken a watan Disambar 2018.
City ta ce “sun yi mamakin” tuhume-tuhumen kuma suna goyon bayan “hujjar da ba za a iya maye gurbin ta da wata ba”.
Hukumar na iya zartar da hukunci tun daga tara da cire maki zuwa kora daga gasar Premier.
Manchester City ta yi mamakin fitar da wadannan zarge-zargen karya da suka saba da dokokin Premier, musamman idan aka yi la’akari da yawan aiki da kuma tarin cikakkun bayanai da aka samar da EPL,” in ji kulob din a cikin wata sanarwa.
A wani labarin kuma: Kafin Karawarsu Da Manchester United, Leeds Ta Sallami Kocinta
Kungiyar Kwallon Kafa ta Leeds United ta sallami kocinta Jesse Marsch. Kamar yadda Daily Post ta ruwaito.
Kungiyar ta sallami kocin ne biyo bayan rashin nasarar da take samu a baya bayan nan.